Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Laraba

24 Agusta 2022

19:12:36
1300636

​Iran: Sojoji Sun Fara Gudanar Da Atisayin Gwada Sabbin Jiragen Yaki Marasa Matuki

Rundunar sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta fara wani gagarumin atisaye na sarrafa jirage marasa matuki da aka kera su da fasaha ta musamman ta zamani, domin kai hare-hare da kuma gudanar da ayyuka na leken asiri.

Wannan atisayen dai ana gudanar ad shia dukkanin bangarori na kasar Iran, daga gabashin kasar har zuwa yammaci, daga kudanci har zuwa arewaci da kuma cikin tekun fasha.

Admiral Seyyed Mahmoud Mousavi, mataimakin babban kwamandan rundunar sojin kasar Iran, kuma mai magana da yawun atisayen na hadin gwiwa a tsakanin dukkanin bangarorin soji na sama da kasa da ruwa, ya bayyana cewa atisayin shi ne irinsa na farko da sojojin Iran suke gudanarwa da ake amfani da jiragen yaki marasa matuki zalla.

Ya kara da cewa, a cikin wannan atisayin ana gwada sabbin jiragen yakin marasa matuki da Iran ta kera, wadanda za su iya daukar makamai masu linzami da kuma kai hari da su daga tazara mai nisan gaske a cikin sararin samaniya.

Ya ce wannan yana zuwa ne domin kara zama cikin shirin ko ta kwana domin fuskantar kowace irin barazana a kan kasar, da kuma mayar da martanin da ya dace a nan take.

342/