Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Laraba

24 Agusta 2022

19:08:45
1300627

​Iran: Shugaban Hukumar IAEA Shi Ne Babbar Mai Kafar Ungulu A Farfado Da JCPOA

Kamfanin dillancin Nournews na kasar Iran ya bayyana cewa shugaban hukuma mai kula da al-amuran makamashin nukliya ta duniya (IAEA) Rafael Grossi, shi ne babban shamaki wanda yake hana farfado da yarjeniyar JCPOA.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Nournews ya na fadar haka a jiya Talata. Ya kuma kara da cewa a hirar da Grossi ya yi da tashar talabijin ta CNN ta kasar Amurka a jiya Talata, ya yi kokarin maida tattaunawar farfado da JCPOA a matsayin wani abu da ke hannunsa, a ciiin hirarsa ta CNN Grossi yace gwamnatin kasar Iran ta ki amincewa hukumarsa ta gudanar da bincike a wasu wurare wadanda ita Iran ta gudanar da binciken kan cinadarin Uranium a cikinnsu.

Kamfanin dillancin labaran Nournews ya kara da cewa shigar da harkokin siyasa wanda Grossi yake yi dangane da tattaunawar ta Vienna yana daga cikin abubuwan da suke maida hannun agogo baya a cii gaban yarjeniyar .

Daga karshe kamfanin dillancin labaran Nournews ya kammala da zargi Grossi da haka dai da HKI don hana farfado da yarjeniyar ta shirin nukliyar kasar Iran ta shekara ta 2015.

342/