Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Laraba

24 Agusta 2022

19:06:39
1300624

Iran Ta Bada Kyautar Allurar Rigakafi Ta Barakat Guda 100,000 Ga kasar Mali

Ministan harkokin wajen kasar Iran Amir Abdallahiyan ya fadi a lokacin taron farko na kwamitin hadin guiwa tsakanin Iran da Mali cewa kasar iran ta mika kyautar Allurar rigakafin cutar korona ta Barakat ga A’lumma da kuma gwamnatin kasar Mali

Taron da minsitocin kasashen wajen kasashen mali da Iran suka gudanar da ya hada da masana tattalin Arziki da manyan yan kasuwa sun bayyana jin dadinsu game da samun damar halartar taron hadin guiwar tsakanin kasashen biyu.

Ya ce ina farin ciki bayan kwashe watanni 6 da kulla yarjejeniya tsakanin mu a birnin Tehran da ta kunshi hadin guiwa da bangarori masu zaman kansu da na gwamnati a fannonin kimiya da fasaha da yawon bude ido lafiya da makamantasu a na cig a da bibiyarsu a kan tsarin da ya dace.

Daga karshe ya nuna cewa gwamnatin Ra’isi ta sanya batun daddiyar alaka mai tarihi dake tsakaninta da Mali a matsayin abinda da ta sanya a gaba kuma ta himmatu sosai wajen ganin an kara karfafa dangantaka tsakaninsu da kuma shirin da take da shi wajen bullo da sabbin hanyoyi na bunkasa dangantaka tsakaninsu,

342/