Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Talata

23 Agusta 2022

16:50:43
1300330

​IRGC: Iran Ta Fara Saida Ingantattun Jiragen Yakin Da Ake Sarrafasu Daga Nesa

Kasar Iran ta fara saida jiragen yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa, kuma a halin yanzu tana daga cikin tsirarun kasashen da suka fi korewa a fasahar keri a irin wadannan jiragen a duniya.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Burgediya Janar Amir-Ali Hajizadeh kwamanda mai kula da bangaren jiragen yaki a rundunar IRGC yana fadar haka a jiya Litinin. Ya kuma kara da cewa yaba da yadda kasar Iran ta sami ci gaba mai yawa a fasahar kera jiragen yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa, ci gaba mai sauri so sai.

Hajizadeh ya ce dakarun IRGC ta sami nasaran da ta samu a wannan bangaren ne tare da taimakon kamfanoni kere-kere masu zaman kansu da kuma jami’o’iin ilmin kimiya na cikin gida.

Kwamnadan ya kara da cewa kasashen yamma wadanda wannan ci gaban bai yi masu dade ba sun bayyana cewa manufar farfado da yarjeniyar JCPOA a wajensu itace takaida hannin kasar wajen samun fasahar kere makamai masu linzami da kuma jiragen yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa.

342/