Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Talata

23 Agusta 2022

16:49:38
1300328

Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Ya Fara Ziyarar Aiki A Kasar Mali

Amir Abdallahiyan minsitan harkokin wajen kasar Iran ya isa birnin Bamako fadar mulkin kasar Mali tare da rakiyar babbar tawagar yan siyasa dam asana tattalin arziki kumaya samu kyakkyawar tarba daga takwaransa na kasar Abdallah Diop.

A lokacin ganawarsu minsitan harkokin wajen kasar Mali ya nuna gamsuwarsa game da ziyarar da takwaransa na kasar Iran ya kawo mali, kuma ya bayyana ziyarar a matsayin kyakkyawar niyar iran na bunkasa alaka tsakaninta da kasar Mali,kuma ya bayyana godiyar gwamnatin kasar kan kulawar da iran ta bayar wajen bunkasa alaka tsakaninsu.

Anasa bangaren minsitan harkokin wajen kasar Iran da yake bayyana siyasar gwamnati na kara kyuatata dangantaka tsakaninta da kasar mali musamman a bangaren ciniki da tattalin arziki , kana ya sanar da shirin da iran take dashi na musamman wajen kara dangantakar kasuwanci da Bamako

Amir Abdallahiyan ya kai ziyarar ne bisa goron gayyatar da takwaransa na kasar Mali ya aike masa lokacin day a kawo ziyara kasar Iran, a nan gaba ministan zai gana da shugaban kasar Mali domin tattaunawa kan yadda za’a bunkasa alaka dake tsakaninsu.

342/