Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Litinin

30 Mayu 2022

11:24:28
1262228

Shugaban Kasar Tajikistan Ya na Ziyarar Aiki Ta Yini Biyu A Birnin Tehran.

Rahotanni sun bayyana cewa shugaban kasar Tajikistan EmamAli Rahmon ya iso birnin Tehran tare da babbar tawaga dake rufa masa baya, bisa gayyatar da shugaban kasar Iran Ibrahim Raisi ya yi masa inda ya samu kyakkyawar tarba daga ministan kula da makamashi na kasar Iran,

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - A ziyarar ta kwanaki biyu zai hada da tattaunawa da shugaban kasar game da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu da kuma rattaba hannun kan yarjeniyoyi da suka shafi tattalin arzki fasaha siyasa da kuma hadin guiwa kan al’adu .

Shugaban kasar Iran Ibrahim Ra’isi ya kai ziyarar kasar Tajikistan a shekarar da ta gabata bisa gayyatar takwaransa na kasar domin halartar taron kasashen shanhai inda kasashen biyu suka rattaba hannu kan yarjeniyoyi na yin aiki tare har guda 8 .

342/