Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Litinin

30 Mayu 2022

11:23:45
1262227

M DD: Afrika Na Fuskantar Matsaloli Saboda Yakin Ukraine

Rahoto da Majalisar dinkin duniya ta fitar ya nuna cewa Nahiyar Afrika na fuskantar rikici da ba’a taba ganin irinsa ba saboda yakin kasahen rasha da Ukrain da ya jawo matsalar karancin Abinci da hauhawan farashin manfetur da iskar gas.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Ta ci gaba da cewa takunkumin da kasashe turai suka kakabawa kasar Rasha ya taimaka sosai wajen kawo cikas wajen samar da Alkama, da takin zamani da sauran kayayyakin bukata na rayuwa, lamarin day a karra ruruta wutar matsalolin da nahiyar Afrika fuskanta daba sauyin yanayi da kuma Annobar cutar Korona.

A gefe guda kuma minsitan harkokin wajen kasar Rasha Sargei Lavrov ya bayyana yantar da yankin Danbas na Ukrain da ya balle a matsayin abin da tafi ba fiffiko ba tare da wani sharadi ba, yana mai cewa sauran yankunan kasar Ukrain suke da alhakin yanke shawara kan makomarsu

Kasar Rasha ta kaddamar da harin soji kan kasar Ukrain ne a wata fabarerun da ya gabata bayan da ta ki yin aiki da yarjejeniyar da aka kulla tsakaninta da rasha da kuma batun amince da yakin Dntesk da Luhanks da suka barke.

342/