Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Litinin

30 Mayu 2022

11:22:01
1262225

​Iran Ta Yi Kira Ga Hadin Kai Don Fada Da Mulkin Wariya Na Isra’ila

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Saed Khadib Zadeh ya yi allawadai da keta hurumin masallacin Al-Aksa wanda yahudawan sahyoniyya suka yi a jiya Lahadi.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Kahdib Zadeh yana fadar haka ya kuma kara da cewa kubutar da masallacin al-aksa shi ne babban al-amarin da ke gaban al-ummar musulmi a halin yansu. Ya kuma kammala da cewa hadin kai da aiki tare ne kawai zai bawa musulmi damar samun nasara a wannan yaki da HKI>

Kafin haka dai a jiya Lahadi ne dubban yahudawan sahyoniyya suka gudanar da abinda suka rika “Jerin gwanon Tutuci”, wanda ya kaisu ga shiga masallacin al-aksa ta gabacin birnin Qudus inda falasdinawa suka fi yawa.

Yahudawan wadanda sukasami rakiyar sojojkin HKI, sun kara da matasa Falasdinawa, a lokacin da suka shiga masallacin suka kuma kori Faladinawa musulmi daga cikin masallacin. Sannan suka ci gaba da ibadunsa a cikinsa. Falasdiawa kimani 145 suka ci rauni saboda harbin bindiga ko wasu makaman da sojojin haramtacciyar kasar suka yi amfani da su.

342/