Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Litinin

30 Mayu 2022

11:17:49
1262220

​Iran Ta Sanar Da Aikewa Da Tawaga Zuwa Saudiyya

Iran ta sanar da cewa wata tawagar kasar ta isa Saudiyya domin tattauna batutuwa da suka shafi aikin Hajji domin saukaka al'amuran alhazan Iran.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Ministan harkokin wajen kasar Iran Hossein Amir Abdollahian ya sanar da cewa, tawagar ta wakilci ma'aikatar harkokin wajen kasar ne domin saukaka jigilar maniyyata aikin hajjin bana.

Hakan ya zo ne a cikin wani bayaninsa da ya yi a yayin wani zaman da ya yi tare da jami’an kuma Hajji da ziyara domin tattauna batutuwan da suka shafi tura maniyyata aikin Hajjin bana.

Ya kara da cewa ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran za ta yi amfani da karfinta wajen jigilar mahajjata da jami'an zartarwa tun daga farkon jigilar maniyyata zuwa karshenta, kuma za ta aike da tawaga ta ofishin jakadanci zuwa kasar Saudiyya don aiwatar da wannan manufa ta hanyoyi na diflomasiyya.

Amir Abdollahian ya bayyana fatansa cewa, tare da goyon bayan jami'an Saudiyya, za a gudanar da ayyukan Hajjin bana cikin natsuwa da kuma nasara.

342/