Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Litinin

30 Mayu 2022

11:16:34
1262218

​Kenya: Tsarin Cinikayya Na Musulunci Na Kara Habaka A Dukkanin Bangarorin Tattalin Arziki

Harkokin Tattalin Arziki na Capital Solutions na musulunci, tare da hadin gwiwa da babbar hukumar fintech ta Kenya, na da shirin samar wa kananan ‘yan kasuwa tallafin kudi da suke bukata don tsarawa da biyan bukatunsu na kudi ta hanyar dandali guda, na samar da wasu kayan aiki da za su taimaka wajen samar da kudade.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - habarta cewa, kasar Kenya daya ce daga cikin kasashe masu tasowa a nahiyar Afirka, ta samu damar janyo hankulan masu zuba jari da harkokin bunkasa tattalin arzikinta, kuma a halin da ake ciki fannin bayar da tallafin kudi na Musulunci yana ci gaba da bunkasa, sakamakon kasancewar al'ummar musulmi a wannan kasa suna baiwa abin muhimmanci.

Baya ga ayyukan bankin Musulunci, hukumomin Kenya kuma suna son yin amfani da FinTech don ciyar da fannin ayyukan bankin musulunci a gaba.

Yin amfani da goyan bayan irin waɗannan sababbin hanyoyi suna sauƙaƙe ma'amaloli da ƙarfafa kasuwanci ga manyan kamfanoni da ƙananan masana'antu da matsakaita, har ma da daidaikun mutane.

An kafa Capital Solutions ne a cikin 2020, kuma a cewar Mohamoud Dualeh, wanda ya kafa kamfanin, yana da niyyar inganta hada-hadar kudi a Kenya, kuma shi ne na farko da ya fara irin wanann aiki a kasar Kenya bisa ka’idojin mu’amalar kasuwanci a bisa tsari na shari’ar muslunci a hukumance.

342/