Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Litinin

30 Mayu 2022

11:14:07
1262216

Iran: Girgizan Kasa Mai Karfin Ma’aunin Richter 4.4 Ta Aukawa Yankin Qasre-Shirin

Cibiyar auna girgizan kasa ta kasar Iran da ke jami’an Tehran ta bada sanarwan cewa girgizan kasa mai karfin ma’aunin Richter 4.4 ta aukawa yankin Qasre–Shirin a lardin Kermanshah a safiyar yau Lahadi har sau biyu.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa girgizan kasar ta auku ne da misalign karfe 10:22 na safe, kuma a kan longitude 45.62 da kuma latitude 34.65.

Zurfin girgizan kasar ya kai kilomita 10 karkashin kasa, har ya zuwa lokacin bada wannan labarin babu wani bayani dangane da asarorin da aka yi na rayuka ko dukiyoyi.

342/