Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Asabar

28 Mayu 2022

15:08:28
1261812

​Iran: IRGC Sun Kwace Jiragen Ruwan Kasar Girka Saboda Maida Martani

A jiya jumma’a ce dakarun kare juyin juya halin musulunci wato (IRGC) suka kwace jiragen kasar Girka guda biyu a cikin tekun farisa.

ABNA24 : ya bayyana cewa kafin haka gwamnatin kasar Girka ta kwace jirgin ruwan kasar Iran dauke da danyen manfetur ta kuma mikawa Amurka jirgin.

Majiyar jaridar ‘Noor Neww’ ta dakarun ta kara da cewa sun kama jiragen ruwan kasar Girka ne saboda sabawa dokokin amfani da tekun farisa.

Jirgin kasar Rasha duke da man fetur na kasar Iran kimani ganga 700,000 girkawa suka kama tare da umurnin gwamnatin Amurka a ranar Alhamis, kuma ta mikawa sojojin Amurka a yankin.

A nata bangaren gwamnatin Amurka tace tana duba lamarin don sanin abinda zata yi kan kame jiragen yakin na Girka wanda IRGC suka yi.

A wani bangaren kuma ma’aikatar sharia ta kasar Amurka ta bada sanarwan cewa tare da umurninta ne kasar Girka ta kama jirgin ruwan kasar Rasha dauke da man fetur na kasar Iran a ranar Alhamis.

342/