Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Asabar

28 Mayu 2022

15:05:16
1261808

APC: A Zaben Fidda 'Yan Takarar Gwamnonin Jihohin Kasar An Zabi Mafi Yawan Gwamnoni Masu Ci

Jam’iyyar APC mai mulki a tarayyar Najeriya ta gudanar da zaben wandanda za su tsayawa jam’iyyar takarar gwamnonin jihohi a zaben shekara ta 2023 a jiya Jumma’a inda mafi yawan gwamnonin masu ci suka sami da mar tsayawa karo na biyu ba tare da wata matsalaba.

Sai da a wasu jihohin an sami sabbin ‘yan takara wanda ya sa bangaren masu adawa suka ki amincewa da sakamakon zaben.

Gwamnonin jihohin Yobe, Zamfara, Borno, Lagos, Gombe da kuma Kwara duk sun wuce ba tare da wata matsalaba. A jihar Rivers wanda dan kasuwa Tonye Cole ya lace zaben dan takarar gwamna a jam’iyyar ta APC.

342/