Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Asabar

28 Mayu 2022

15:04:37
1261807

​Wata Kotu A Tunisia Ta Fidda Sammancin Hana SHuwagabannin Jam’iyyun Siyasar Kasar Fita

Wata majiyar ma’aikatar sharia a kasar Tunisa ta bada labarin cewa wata kotu ta fidda sammacin hana shuwagabannin wasu jam’iyyun siyasar kasar daga ciki har da Rashid Ghanishi na jam’iyyar Annahda ta masu kishin addinin.

ABNA24 : Amma Ghanushi ya bayyana cewa bai da labarin wannan sammashin har ya zuwa lokacin hada wannan rahoton. Tun shekarar da ta gabata ce shugaba Kais Sa'eed ya kwaci iko da jan ragamar shugabancin kasar bayan da ya rufe majalisar dokokin kasar kuma yayi alkawalin zai sauyi kundin tsarin mulkin.

Tun lokacin ne kuma ya shiga takun saka da jam'iyyun siyasar kasar , musamman Jam'iyyar Annahda ta Rashid Ganushi ta masu kishin addini.

342/