Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Asabar

28 Mayu 2022

15:03:23
1261805

​Abdollahian: An Samu Ci Gaba A Tattaunawa Tsakanin Iran Da Saudiyya

Ministan harkokin wajen kasar Iran Hossein Amir Abdollahian ya fada a jiya Alhamis cewa: Iran da Saudiyya manyan kasashe biyu ne masu tasiri a yankin, kuma Tehran ba ta yanke huldar jakadanci da Riyadh gaba daya ba.

Ministan harkokin wajen na Iran ya yi nuni da cewa, an samu ci gaba a tattaunawar da aka yi tsakanin kasarsa da Saudiyya, inda ya yi maraba da komawar dangantakar hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu kamar yadda take a baya.

Ministan na Iran ya yi nuni da cewa, yayin da tatatunawarsu Riyadh ke kara samun ci gaba, dangantakar za ta dawo daidai, wanda kuma akwai yiwuwar ya gana da takwaransa na Saudiyya, Faisal bin Farhan a wata kasa ta uku nan ba da jimawa ba.

A yayin halartar taron Davos na duniya, ministan harkokin wajen Saudiyya ya bayyana cewa: A Masarautar da GCC, muna mai da hankali kan makomar tsaro da hadin gwiwa, kuma hannayenmu a bude suke ga dukkan kasashe, da kuma Iran.

Shi ma Ministan harkokin wajen Saudiyya ya bayyana cewa, an samu wasu ci gaba a tattauawarsu tare da Iran, amma bai isa ba, yana mai bayyana cewa akwai bukatar ci gaba da fadada tattaunawar domin cimma burin da ake bukata.

342/