Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Alhamis

26 Mayu 2022

20:10:35
1261289

Iran Ta Gayyaci Jakadan Kasar Girka A Tehran Kan Kama Jirgin Ruwanta

Ma’aikatar harkokin wajen kasa iran ta gayyaci mai kula da ofishin jakadancin kasar Girka a nan Teheran saboda jakadanta din baya nan, domin nuna rashin amincewa game da kama jirgin ruwa mai dauke da tutar iran da aka yi a ruwan Girka,

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Awajen taron direktan kula da bangaren Tekun Medeteranea a ma’aikatar harkokin wajen kasar iran ya tunatar da kasar Girka game da nauyin day a wajaba akanta a mataki na kasa da kasa, duk da yake cewa jirgin ya tsaya ne saboda da wasu matsalolin naura da aka samu, kana kuma yayi soki kasar Girka game da mika wuya da ta yi kan matsin lambar Amruka kan wannan batun,

Ya kara da cewa tsayar da jirgin ruwa na daukar kaya dake dauke da tutar kasar iran misali ne na fashin teku, wanda Athensa da sauran wadanda ke da hannun wajen kwace jirgin ruwa ba bisa kaida ba suke da alhakin duk abin da ya biyo baya. Don haka kasar Iran ba za ta yi kasa a guiwa wajen kare hakkokinta ba, kuma tana fatan kasar Girka za ta yi aiki da Alkawuran da ta dauka na safara jiragen ruwa .

Daga karshe mai kula da ofishin jakadancin na kasar Girka ta tehran ya ce zai isar da sakon kasar iran ga gwamnatin kasarsa.

342/