Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Alhamis

26 Mayu 2022

20:08:27
1261287

Gobara ta Tashi A Tashar Jirgin Ruwan Sauakin A Tekun Bahar Maliya A kasar Sudan

A jiya labaran Wata gobara mai karfi ta tashi a tashar jirgin ruwa na Suakin dake tekun bahar maliya a kasar Sudan, babbar hanyar kasuwanci ta kasahen gabashin Afrika da tekun bahar maliya. Sai dai tuni a aka shawo kanta kuma komai ya lafe sai dai an fara gudanar da bincike domin gano musababbin tashin gobarar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Ita dai tashar jirgin ruwa ta bahar maliya ta kasar Sudan wata cibiyace ta fita da shigo da kayayyaki daga kasahen Sudan Chadi Habash da Afrika ta tsakiya da kuma man fetur daga kasar Sudan ta Kudu

A karshen shekara ta 2017 ne tsohon shugaban kasar Sudan Umar ALbashir ya rattaba hannu kan yarjejeniyar shekaru 99 tsakaninsa da shugaban kasar Turkiya Dayyib Rajab Ardogan domin sake gina tashar jirgin ruwa ta Suake musamman dun kula da tsoffin gine-gine da ke wajen da aka yi su run zaman fur’auna Ramases na 2

Kasar sudan ta yi ra kashe 40 cikin 100 na kudadenn shigarta a watan Oktoba bayan da hukumomin kasa da kasa suka suke tallafin da suke basu saboda mayar da martani kan juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar karkashin jagorancin Janaral Abdel fatah Alsisi.

342/