Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Alhamis

26 Mayu 2022

20:04:23
1261285

​ Afrika Ta Kudu : An Yi Zanga Zangar Kyammar Faransa A Nahiyar

A Afrika ta Kudu, kungiyoyi da dama ne masu rajin ‘yanci da ra’ayin kishin Afrika, suka gudunar da wata zanga zangar nuna kin jinin faransa a nahiyar Afrika.

Masu zanga zangar dake raira taken kin faransa, sun taru ne a gaban ofishin jakadancin faransa a Afrika ta kudun jiya Laraba a dalilin zagayowar ranar Afrika.

Daruruwan masu zanga zangar suna masu kalubalantar faransar akan kasancewarta a Afrika, da batun kudin bai daya na CFA, da sansanonin sojinta da kuma tasirinta kan shugabannin nahiyar, da kuma kawo karshen amfani da harshen faransanci a hukumance a Afrika.

Masu zanga zangar sun hada da ‘yan kasashen Afrika ta Kudu, Congo, kamaru, da kuma ‘yan Mali.

Daga karshe masu zanga zangar sun mikawa jakadan na faransa wasu takardun jerin bukatunsu, inda suka baiwa faransar wa’adin kwanaki 14 na yi musu bayyani ko kuma su dauki wasu matakai na takawa salon mulkin mallakar da take ci gaba da amfani da shi a nahiyar.

Kin jinin faransa dai na dada kamari a Afrika, inda ko a makon da ya gabata wasu kungiyoyi suka gudanar da zanga zangar kin jinin faransa karon farko a kasar Chadi.

A kasashen Mali da Burkina faso dama zanga zangar kin jinin faransa ta zama ruwan dare, yayin da a Jamhuriyar Nijar yunkurin kungiyoyin fara na gudanar da irin wannan zanga zanga ke cin karo da haramcin mahukunta a kasar.

342/