Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Alhamis

26 Mayu 2022

20:03:08
1261284

AU : Rikicin Ukraine Ya Wargaza Daidaiton Dake Akwai Tsakanin Sassan Duniya

Shugaban hukumar gudanarwar kungiyar tarayyar Afirka ta AU Moussa Faki Mahamat ya bayyana cewa, rikicin Ukraine ya wargaza daidaiton dake akwai tsakanin sassan yankunan duniya.

Mista Mahamat, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa kasashen nahiyar Afirka na matukar dandana kudar su, sakamakon mummunan tasirin rikicin dake gudana tsakanin Rasha da Ukraine.

Hakan ya kuma dada fito da raunin tsarin tattalin arzikin Afirka a fili.

Jami’in ya ce wannan rikici, ya tauye damar da ake da ita ta fitar da amfanin gona zuwa sassan duniya, ya kuma ta’azzara hauhawar farashin kayayyakin abinci.

Ya ce baya ga kalubalen sauyin yanayi, da annobar COVID-19, rikicin Ukraine ya sake ingiza matsalolin karancin cimaka da duniya ke fama da shi.

Wani rahoto da shirin samar da ci gaba na MDD ko UNDP ya fitar a ranar Talata, ya yi gargadin cewa, rikicin Ukraine na iya kara tsananta koma bayan ci gaban kasashen Afirka, kasashen da tuni suke shan matsi daga tasirin annobar COVID-19.

342/