Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Alhamis

26 Mayu 2022

19:53:40
1261280

​Equatorial Guinea : An Bude Taron Sharar Fage Na Taron Kolin Kungiyar AU

A jiya ne aka bude taron sharar fage na taron kolin kungiyar Tarayyar Afirka a birnin Malabo na kasar Equatorial Guinea.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - A lokacin da yake gabatar da jawabin bude taron ga majalisar zartarwar kungiyar, shugaban gudanarwa na kungiyar Moussa Faki Mahamat ya ya bayyana cewa, taron zai mayar da hankali akan ayyukan jinkai da yaki da ta’addanci da kuma dakile juyin mulkin da sojoji ke yi a wasu kasashen nahiyar.

Ya ce, daga cikin mutane miliyan 113 da ke bukatar taimakon jinkai, miliyan 15 na bukatarsa cikin gaggawa ba tare da bata lokaci ba, wanda kuma hakan ne yasa za a kaddamar da gidauniyar taimakawa irin wadanan mutane a wajen wannan taro.

A sanarwar da gwamnatin Guinea ta bayar ta ce tana sa ran halartar akalla shugabanin kasashen Afirka 20 da kuma wakilai na kasashe daban-daban, wanda kuma bayan taron shararar fagen, a gobe Juma’a ne za a gudanar da taron kolin wanda shugabannin kasashe da shugabannin gwamnatoci za su halarta.

shugaban gudanarwa na kungiyar Moussa Faki Mahamat ya ya bayyana cewa akalla mutane miliyan 30 aka tilastawa barin matsugunan su sakamakon tashe tashen hankula, kuma sama da miliayn 10 daga cikin su yara ne kanana wadanda ke kasa da shekaru 15 a cikin kasashen nahiyar Afirka.

Kimanin mutane miliyan 282 ne ke fama da matsalar karancin abinci mai gina jiki daga cikin mutane kimanin biliyan daya da rabi da ke rayuwa a Afirka a cewar Hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya.

342/