Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Alhamis

26 Mayu 2022

19:49:13
1261278

Senegal: ​Jarirai 11 Ne Suka Rasu A Wata Gobara Da Ta Auku A Wani Asibiti A Yau

Kafofin yada labaran kasar Senegal sun bayar da rahotanni a safiyar yau Alhamis cewa jarirai 11 ne suka mutu a gobarar asibitin Mam Abdoulaziz Si Dabakh da ke Tifuan.

Shugaban kasar Senegal Macky Sall ya wallafa a shafinsa na Twitter a shafinsa na Twitter yana mai cewa: "Na ji radadin mutuwar jarirai 11 a gobarar da ta afku a sashen kula da lafiyar yara na asibitin Mam Abdoul Aziz Si Dabakh da ke Tifuan."

Macky Sall ya kara da cewa, ina mika sakon ta’aziya da juyayi zuwa ga uwayensu da iyalansu."

A nasa bangaren, tsohon dan wasan Senegal El Hadj Diouf ya wallafa a shafinsa na twitter inda ya bayyana cewa: “Yanzu na samu labarin mutuwar jarirai 11 da suka mutu a asibitin Mam Abdelaziz Si Dabakh da ke Tifuan, bayan da wata gobara ta tashi, ya ce muna cikin bakin ciki da kidima kana bin da ya faru.

‘Yan kwana-kwana sun yi kokari wajen kashe gobarar, sannan kuma tuni jami’an tsaro suka shiga gudanar da bincike kan lamarin, domin gano musabbabin abin da ya faru.

342/