Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Laraba

25 Mayu 2022

18:12:12
1260905

​Rasha: Iran Zata Samar Da Wasu Bukatun Rasha A Halin Da Ake Ciki

Mataimakin Firai ministan kasar Rasha Alexander Novak ya bayyana cewa kasar Iran tana da zarafin wadatar da kasar Rasha da wasu bukatunta a dai dai lokacinda makiyan kasar daga kasashen Turai da Amurka suka juya mata baya.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - kasar Iran ya bayyana cewa, Alexander Novak ya fadi haka ne bayan taron hadin guiwa tsakanin kasashen biyu wanda aka gudanar a nan birnin Tehran a safiyar yau Laraba.

Alexander Novak yajagoranci wata tawagar jami’an gwamnati da ‘yan kasuwa masu yawa zuwa nan Tehran don halattar taron nay au, da kuma fatan kara zurfafa dangantaka ta kasuwanci tsakanin kasashen biyu.

Alexander Novak ya ce a shekarar da ta gabata yawan harkokin kasuwanci tsakanin Iran da Rasha ya karu da kashi 81% wanda ya kai dalar Amurka billiyon 4. Kuma akwai damar da kuma hasashen za’a iya kara fadada shi.

A nashi bangaren ministan man fetur na kasar Iran Javad Owji ya bayyana cewa dangantakar kasuwanci tsakanin kasashen biyu zai iya karya takunkuman tattalin arzikin da kasashen yamma suka dorawa kasashen biyu.

342/