Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Laraba

25 Mayu 2022

18:10:04
1260903

Tunisia: Mutane 75 Suka Bace Bayan Da Kwale-Kwalensu Ya Kifa A Cikin Tekun Kasar Tunisia

Rahotanni da suke fitowa daga kasar Tunisia sun bayyana cewa mutane 75 ne suka bace a cikin tekun Medeteranian a yau Laraba bayan da kwale-kwalen da ke dauke da su ya kifa a cikin Tekun.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - nakalto majiyar hukumar ‘yan gudun hijira ta MDD da kuma jami’an tsaron bakin ruwa na kasar Tunisia suna fadar haka. Sun kuma kara da cewa an ceci mutane 24 daga cikin wadanda suke cikin kwale-kwalen.

Labarin ya kara da cewa kwale-kwalen ya taso ne daga garin Zawara ba kasar Libya da nufin ratsa tekun Medeteranina zuwa kasar Italiya, amma sai ya kife a Sfx kusa da bakin ruwa na kasar Tunisia a yau Laraba.

Har yanzun ana ci gaba da neman wanda ke da sauran shan ruwa daga cikin mutane 75 da suka bace.

A shekara ta 2021 da ta gabata dai ‘yan gudun hijira kimani 123,000 suka isa kasar Italiya daga kasashen arewacin Afirka. Wanda ya fi na shekara ta 2020 inda dubu 95 ne suka sami damar karasawa zuwa kasar ta Italiya. Da dama sun halaka a cikin ruwan tekun Medeteranina.

342/