Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Laraba

25 Mayu 2022

18:09:23
1260902

​Najeriya: IPOB Ta Yi Tir Da Kisan Wata Bahaushiya A Jihar Anambra

Kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra IPOB, a ranar Talata, ta yi Allah wadai da kisan wata mata mai dauke da juna biyu ‘Yar Jihar Adamawa da ‘Ya’yanta hudu.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - A rahoton da jaridar Leadership ta bayar, matar ‘yar asalin jihar Adamawa ce da ke zaune a Orumba ta Kudu a jihar Anambra, a ranar Lahadin da ta gabata ne ‘yan bindigar suka yi wa mutanen da ba su ji -ba gani ba hari a yankin Kudu-maso-Gabas.

An kashe ta ne tare da ‘ya’yanta hudu amma direban babur din da ke dauke da ita ya tsere bayan kai harin.

Kazalika a wannan ranar an kashe mahaya babura 5 ‘yan kasuwa tare da kona kekunansu a karamar hukumar Onocha.

An ajiye gawarwakinsu a dakin ajiyar gawa yayin da na biyar ya kone kurmus.

Da take mayar da martani game da hare-haren da aka kai wa Hausawan a Kudu maso Gabas, kungiyar IPOB, ta bakin mai magana da yawunta, Emma Powerful, ta ce ‘yan Arewa suna shan wahala sosai, kuma ba su cancanci a kai musu hari ba.

“Muna sake jaddada cewa Hausawa suna shan wahala sosai a hannun Fulani kamar mutanen Biafara, don haka ba za mu bari wani mai laifi ya sake taba su ba. Suna da ‘yancin yin kasuwancinsu a duk inda suka ga dama a kasarmu.”

“Wadanda suka kashe matar nan da ’Ya’yanta hudu Hausawa, dole ne su fuskanci hukuncinsu, su jira mu, zamu zo kansu” in ji sanarwar IPOB.

342/