Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Laraba

25 Mayu 2022

18:04:58
1260897

Amurka : Matashi Ya Hallaka Mutum 21 A Wata Makarantar Firamare

Hukumomi a binrin Texas na Amurka sun ce mutane 21 suka mutu ciki har da yara 18 a wani harin bindiga da wani matashi ya kai a wata makarantar firamare ranar Talata.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Wanda ake zargin matashi dan shekara 18, ya yi wa yara 18 da wani malami kisan walakanci a garin Uvalde, kamar yadda gwamnan jihar Texas Greg Abbott ya shaida a yayin wani taron gaggawa.

Baya ga wadanda suka mutun da akwai dalibai sama da goma dake kwance a asibiti.

Wanda ake zargi da harbin mai suna Salvador Ramos, shi ma an bindige shi.

An yi zargin cewa kafin ya kai harin a makarantar, matashin ya harbe kakarsa.

Harin makarantar firamarin ta Robb, ya kasance daya daga cikin mafi muni a makaranta tsawon shekaru a Amurka.

Kawo yanzu ‘yan sanda na bincike kan dalilin matashin na kai wannan harin, a yayin da shugaban kasar Joe Biden, ya dawo da muhawarar da aka jima anayi a kasar game da batun mallakar bindiga.

342/