Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Laraba

25 Mayu 2022

18:00:33
1260893

An Sake Zaben Dr Tedros A Matsayin Darakta-Janar Na WHO

Kasashe mambobin hukumar lafiya ta duniya sun sake zaben Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus don yin wa'adi na biyu na shekaru biyar a matsayin Darakta-Janar na hukumar (WHO).

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Dr Tedros, wanda ya rike da shugabancin hukumar tun cikin shekarar 2017, an tabbatar da sake zabensa a yayin babban taron hukumar kiwon lafiya ta duniya karo na 75 a Geneva.

Kuma shi ne dan takara tilo, da ya tsaya takarar zaben.

Bayan zabensa Dr Tedros ya ce "Na gamsu da damar da kasashe mambobin kungiyar suka ba ni na yin wa'adi na biyu a matsayin Darakta-Janar na WHO."

Ya kara da cewa Wannan karramawa, ta za bashi damar himmatuwa wajen yin aiki tare da dukkan kasashe, abokan aiki da na hulda na hukumar, don tabbatar da cewa WHO ta inganta kiwon lafiya, da kuma hidima ga marasa galihu. ”

Sabon wa'adin Dr Tedros zai fara a hukumance a ranar 16 ga watan Agusta 2022.

342/