Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ABNA24
Talata

24 Mayu 2022

19:48:48
1260596

Ayatullah Ramezani: Kalmar "Allah Ne Ya 'Yantar Da Khorramshahr" Tana Da Batutuwa Da Dama Akarkashinta / Imam Khumaini (R.A) Ya Na Ganin Ikon Ubangiji A Cikin Dukkan Al'amura.

Babban Shugaban Majalisar Ahlul-Baiti (AS) Ta Duniya ya ce: Imam Khumaini (RA) ya ga goyon bayan Ubangiji da ikonsa cikin lamarunsa, wannan wani abu ne da ya kamata a hankali mutane su cimmawa, wannan Furuci na (Allah ya 'yantar da Khorramshahr), yana dauke da kalmomi da dama. kuma akwai abubuwa da yawa da za a yi bayani akai karkashin sa.

Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti (AS) - Abna – yakawo rahoton cewa: Ayatullah "Reza Ramezani" a safiyar jiya Litinin 23 ga watan Mayu shekara ta 2022 a wani taron na darasin Akhlaq a tsakanin daliban jami'ar Ahlul Baiti (AS) yana mai nuni da cewa. dangane da tasirin samuwar tsarin tauhidi, ya bayyana cewa: Alokacin da ya zamo mutum yana cikin tsarin tauhidi, a hakikanin ma’anar Kalmar to zai zama mai tauhidi, tauhidi yana dauke da matakai uku ne, tauhidi na zahiri, tauhidi na ayyuka da tauhidi na sifah, to masanin tauhidi zai iya kaiwa ga matakin da zi iya narkewa acikin sa, zai zamo ya narke ackin tuhidin ayyuka da tauhidin Siffofi, sai ya zamoa karshe baya iya ganin kansa ko tantance ta, kuma ya zamo baya iya ganin kansa amatsin komai, bisa maganar Imam Sadek (AS) da ya ke cewa: ni ne mafi kankanta kuma ni birbashi ne kawai, haka mutum yake ganin kansa.

Ya ci gaba da cewa: Kalmar (Allah Akbar) ba kawai tana nufin Allah ya fi komai girma ba ne, a’a tana nufin Allah ya girmama ga abin da za a iya siffanta shi da shi, in ba haka ba idan muka ce Allah ya fi komai girma kamar yadda Imam Sadek (AS) ya fada, mun takaita Allah ne Kenan, domin kuwa mun sanya Allah a cikin matakin sauran halittu. Ta wannan mahangar, idan mutum ya lura da sararin duniya ya ga kansa kuma alhali yana da kallo na Ubangiji, to a wannan lokacin zai nazarci abubuwan da suka faru da abubuwan da suke faruwa daidai da daidai.

Babban Shugaban Majalisar Ahlul-Baiti (AS) Ta Duniya ya kara da cewa: A bisa wannan mahangar Marigayi Imam ya kasance masanin fikihu, masani halayya, malami, jagora kuma sufi wanda yake ganin duniya ta nazari na musamman ta kowace fuska." Imam a matsayinsa na sufi yana ganin ikon Ubangiji dangane da al'amura a ko'ina kuma ba shi da wani iko a kan ikon Ubangiji, amma duk wadannan siffofi ne nasa. A mahangar tauhidi, ba za mu iya cewa Allah na da iko aki kuma wasu kuma suna da iko akai ba, kwta-kwata ma bai dace ba mu kwatanta ikon wasu akan ikon Allah ba, Domin ikon Allah shine ikon da kan kansa, kuma ya ke da iko kaitsaye karara.

Ayatullah Ramezani yayin da yake ishara da sirrukan ikon Ubangiji a duniya yana mai cewa: A cikin Alkur'ani mai girma akwai batutuwai guda biyu, daya dangane da mayaka, daya kuma dangane da manzon Allah (SAW), Alkur'ani ya ce game da mayaka, cewa (ba ku ne kuka kasha su ba, Allah ne ya kashe masu mulkin kama karya da karya masu ketara iyaka da azzalumai), domin ya bayyana ikon Allah a nan. Haka nan Alkur’ani ya ce game da Manzon Allah (S.A.W) cewa ba ka yi harbi ba lokacin da ka harbi, amma Allah ne ya ba ka wannan iko yin wannan harbin. Wannan mahangar tana da matukar muhimmanci, malaminmu ya kasance yana cewa Allah yana girmama Annabi a nan wajen, yana cewa ba kai kayi harbin ba, sai dai mu ne muka harba shi, wannan batun ba a anbaceshi ga mayaka ba a cikin Alkur'ani, kuma Allah ya yi amfani da wannan tawili wajen girmama shi Annabi (SAW) ne.

Ya ci gaba da cewa: A cikin Khorramshahr akwai mujahidai masu ikhlasi da yawa kuma shahidai da dama ne suka yi shahada a aikin ‘yantar da wannan gari, amma Imam Khumaini (r.a) inda yake son ya yi bincike na sufanci sai ya ce: (Allah ya ‘yanta Khorramshahr). Allah ya sanya acikin zuciyar wannan Mujahid kuma ya kimsa masa irin wannan karfi da makiya suka yanke kauna da shi, wani lokacin wannan ikon ya na tabbata da fadar Allahu Akbar wani lokacin kuma sai anyi wani shiri kana wanda yake kunshe acikin kwakwalen masu yin jihadin, to wannan iko na Allah shine ubangjij ya bayyana shi ta hanyar nasarar da suka samu.

Babban Shugaban Majalisar Ahlul-Baiti (AS) Ta Duniya ya kara da cewa: A cikin labarin Annabi Musa (AS) da ya shiga cikin teku kuma a bayansa akwai rundunar Fir'auna, sun gaya wa wannan annabin cewa tamu ta kare fa. kuma ba za mu iya tsira ba, kuma zamu shude kenan, a nan Annabi Musa (AS) ya nuna tunaninsa na tauhidi cewa tamu bata kare ba, sai dai ayanzu ne ma aikinmu ya fara, Allah yana tare da ni kuma ya taimake ni kuma ya shiryar da ni, ya kuma nuna mana yadda zamuyi, shi yasa nan take su ka ga teku ya tsage, Musa da mutanensa suka tsira, amma da rundunar Fir’auna ta kai tsakiyar teku, sai suka nutse.

Ya yi nuni da cewa: Imam Khumaini (r.a) yana da wannan karfin nazari inda yakasance alokacin dukan karfi na masu girman kai na yankin gabas da kasashen yamma, suka ce ba za su iya yin kuskure ban a iya yakar wannan sauyi ba, wannan yana da matukar muhimmanci, mun ga cewa wadannan ma'abota karfi ne tare da dukkan makircin da suka yi amfani da su, a karshe dai sun kasa karya lagon yunkurin Imam. Marigayi Imam ya ga irin wannan goyon baya da karfi na Ubangiji, wannan wani abu ne da ya kamata a hankali mutane su kai gare shi, wannan jumla ta Imam da yake cewa: (Allah ne ya 'yantar da Khorramshahr), tana da abubuwa da dama karkashinta wanda yakamata ace an iya yin Magana ta musamman dangane da ita.