Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Talata

24 Mayu 2022

19:45:39
1260595

Za’a Gudanar Da Taro Kan Makamashi Tsakanin Iran Da Rasha A Tehran

Kasashen Iran da Rasha za su tattaunawa kan batun makashi a taron da zasu su alokacin ziyarar da mataimakin fira ministan kasar Rasha Alexanda Novak zai kawo nan Tehran tare da babbar tawaga da yake jagoranta

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - A yau ake saran Alexanda zai iso nan birnin Tehran domin halartar taron tsakanin kasaheb biyu kana bin day a shafi makamashi, kasahen Iran da rasha suna da arzikin man fetur da iskar gas mai yawa, kuma suna ji da matsayin babba a siyasar duniya, kuma kasashen suna iya sauya akalar makamashi da tattalin arzikin duniya

A ziyarar da minsitan manfetur na kasar iran Javad Owji ya kai birnin mosko a ranar 18 ga watan Janerun shekara ta 2022, ya ce an dauki kyakkyawan mataki na bunkasa man fetur da filiyan Gas a tudu , da matatun mai da dangoginsu dake karkashin ruwa , da kuma isar da kayan aik da fasaha dake taka muhimmiyar rawa a a bangaren iskar gas na iran.

342/