Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Talata

24 Mayu 2022

19:38:35
1260588

Bankin AfDB, Ya Ware Dala Biliyan Guda Da Rabi Domin Taimakawa Jama’ar Nahiyar

Bankin raya kasashen Afirka na AfDB ko BAD ya amince da ware Dala biliyan guda da rabi a matsayin agajin gaggawa domin taimakawa jama’ar nahiyar wajen shawo kan matsalar karancin abinci sakamakon yakin Ukraine.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Shugaban Bankin Akinwumi Adeshina ya ce akalla manoma miliyan 20 dake Afirka zasu amfana daga wannan shiri domin noma tan miliyan 30 na abinci iri iri da suka hada da alkama da masara da waken soya wadanda ake shigo dasu daga Ukraine.

Yanzu haka farashin abinci da takin zamani a Afirka sun tashi sakamakon mamayar da Rasha ta yiwa Ukraine.

Yau Talata ne ake bude babban taron bankin na raya kasashen Afrika a birnin Acra na Ghana, bayan shafe shekaru biyu a jera ba’a gudanar ba sai ta kafar bidiyo sakamakon annobar korona.

342/