Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Talata

24 Mayu 2022

19:35:52
1260586

Jamus Ta Amince Da Shirin Tsawaita Aikin Sojinta A Nijar

Shugaban gwamnatin Jamus, ya shaida cewar majalisar dokokin kasarsa ta amince da shirin tsawaita aikin da sojin ta ke yi a Nijar na bada horo akan yaki da ta’adanci.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Olaf Scholz, ya bayyana hakan ne yayin ganawa da shugaban kasar ta Nijar, Mohamed Bazoum a ziyarar da ya kai Yamai jiya LItini.

Shugaban gwamnatin Jamus yace zasu zuba ido suga abinda hali zai yi nan gaba dangane da dangantakar kasashen biyu, yayin da ya yaba da ci gaban da ake samu duba da wahalar da ake fuskanta wajen matsalar tsaro a Yankin Sahel.

Scholz ya kuma tabbatar da cewar Jamus zata ci gaba da aiki a rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya (MINUSMA) dake yaki da Yan ta’adda a Mali.

Yayin karbar Scholz a Birnin Yamai, shugaba Bazoum ya jinjinawa hadin kan kasashen biyu.

Gabannin zuwansa Nijar dai, Scholz ya ziyarci kasar Senegal inda ya tattauna da shugaban kasar Macky Sall kan batutuwan da suka shafi tsaro a Afirka da kuma yakin da Rasha ke yi a kasar Ukraine.

Scholz, zai karkare ran gadin nasa a nahiyar da Afrika ta Kudu.

342/