Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - kasar Iran ya bayyana cewa shugaban ya sami tarban sabon sarkin Omma Sultan Haitham bin Tarq Assa’eed.
Labarin ya kara da cewa bayan isarsa sarkin yayi masa tarba na musamman a fadan Al-Alam da ke birnin Muscat sannan shugabannin biyu suka gana, suka kuma tattaunawa batutuwa daban-daban daga cikin har da kyautata dangantaka tsakanin kasshen biyu.
Har’ila yau kafin ya kammala ziyararsa ta kwana guda a birnin Muscat Iran da Omman zasu rattabahannu a kan yarjeniyoyi da dama, sannan shugaban Ra’isa zai gana da Iraniyawa ma zauna kasar Umma.
Har’ila yau akwai ganawa ta musamman tsakanin shugaban da kuma yan kasuwan kasar Omman inda a lokacin ganawar zai bukaci yan kasuwan su zuba jari a kasar Iran su kuma shiga harkokin kasuwanci daban-daban da iraniyawa don amfanin bangarorin biyu.
342/