Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Litinin

23 Mayu 2022

16:40:21
1260179

​Iran: Shugaba Ibrahim Ra'isi Ya Isa Kasar Omman Don Ziyarar Kwana Guda

Shugaban kasar Iran Syyid Ibrahim Ra’isi ya isa birnin Muscat babban birnin kasar Omman a safiyar yau Litinin.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa shugaban ya sami tarban sabon sarkin Omma Sultan Haitham bin Tarq Assa’eed.

Labarin ya kara da cewa bayan isarsa sarkin yayi masa tarba na musamman a fadan Al-Alam da ke birnin Muscat sannan shugabannin biyu suka gana, suka kuma tattaunawa batutuwa daban-daban daga cikin har da kyautata dangantaka tsakanin kasshen biyu.

Har’ila yau kafin ya kammala ziyararsa ta kwana guda a birnin Muscat Iran da Omman zasu rattabahannu a kan yarjeniyoyi da dama, sannan shugaban Ra’isa zai gana da Iraniyawa ma zauna kasar Umma.

Har’ila yau akwai ganawa ta musamman tsakanin shugaban da kuma yan kasuwan kasar Omman inda a lokacin ganawar zai bukaci yan kasuwan su zuba jari a kasar Iran su kuma shiga harkokin kasuwanci daban-daban da iraniyawa don amfanin bangarorin biyu.

342/