Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Litinin

23 Mayu 2022

16:38:50
1260177

​Senegal: Jamus Zata Hada Kai Da Senegal Wajen Bunkasa Aikin Hakar Gas A Na kasar

A kokarin da gwamnatin kasar Jamus take yin a rage dogaro da iskar gas na kasar Rasha, shugaban kasar Olaf Scholz wanda ya kammala ziyarar aiki a kasar Senagal a ranar Lahadi ya bayyana cewa gwamnatin kasar a shirye take ta hada kai da kasar Senegal wajen bunkasa ayyukan hakar isakar gas da kuma makamshi mai tsabta kamar na iska da kuma hasken rana.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - nakalto Olaf Scholz yana fadar haka a jawabin hadin guiwa da ya gabatar tare da shugaban kasar Sengal Maky Sall a jiya Lahadi.

An yi has ashen cewa yawan isakar gas wanda kasar Senegal zata fitar a shekara mai zuwa zai kai ton miliyon 2.5, sannan zuwa shekara ta 2030 yawan zai kai ton miliyon 10.

342/