Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Litinin

23 Mayu 2022

16:33:29
1260171

​Ministan Harkokin Wajen Mali: Ba Mu Gaba Da Faransa, Amma Dole Ne Ta Mutunta ‘Yancinmu

Ministan harkokin wajen Mali Abdallah Diop ya ce kasarsa ba tana cikin halin kiyayya da gaba da Faransa ba ne, kuma ba ta rufe kofar tattaunawa da ita ba, yana mai nuni da irin yarjeniyoyi na hadin gwiwar soji da kasar Mali ta kulla da Rasha.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Ministan harkokin wajen Mali Abdallah Diop, ya jaddada cewa rigima da Faransa rigima ce ta siyasa, wanda kuma Mali ba ta bukatar hakan.

Diop ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da kamfanin dillancin labaran Sputnik na kasar Rasha, inda ya ce : "Ba mu rufe kofar tattaunawa ba, kuma kasar Mali ba ta taba yunkurin kai wa sojoji ko kadarorin Faransa hari ba.

A kan haka ya ce ba tana cikin halin kiyayya da Faransa ba ne, abin da Mali ke bukata shi ne Faransa ta mutunta ‘yancinta da mutunta juna.

Kuma Diop ya ci gaba da cewa: "Babban burinmu shi ne tabbatar da ‘yancinmu na siyasa, ta yadda babu wani mahaluki da zai gaya wa Mali da wane bangare ne kawai za ta yi mu’amala, zabin hakan ga kasar ne kawai da al’ummarta, ba tare da katsalandan na kasashen ketare ba.

Tun a ranar Asabar da ta gabata ce ministan harkokin wajen kasar ta Mali ya fara gudanar da wata ziyarar aikia birnin Moscow na kasar Rasha, inda aka rattaba hannu kan yarjeniyoyi daban-daban tsakanin gwamnatocin Mali da Rasha, kan lamurra da suka shafi siyasa, tsaro, cinikayya da tatatlin arziki da kuma batun makamashi.

342/