Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Litinin

23 Mayu 2022

16:31:57
1260169

Iran Ta La’anci Kisan Kanal Hassan Sayyad Khodaei

Iran ta bakin kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar, ta yi allawadai da harin ta’addancin da ya yi sanadin mutuwar wani kanal din rundinar kare juyin juya halin musulinci na kasar.

Saeed Khatibzadeh, ya danganta harin da na makiyan Iran, wanda kuma ya ce zasu dandana kudarsu game da wannan aika aikar.

Irin wannan zubar da jinin, ba ya haifar da komi face kara hadin kan al’ummar Iran game da makircin makiya ma’abotan girman kai, inji shi.

Khatibzadeh, ya kuma isar da sakon ta’aziyya ga iyalan mamacin yana mai kuma yi masa fatan samun rahamar ubangiji.

Jiya Lahadi, wasu mutum biyu kan babur suka harbe kanal Hassan Sayyad Khodaei, a daidai lokacin da ya koma gidansa dake gabashin Tehran babban birnin kasar.

342/