Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Lahadi

22 Mayu 2022

19:27:01
1259878

​An Kashe Wani Daga Cikin Dakarun Kare Juyin Musulunci Na Iran IRGC A Nan Tehran

Rahotanni da kamfanin dillancin labarai na IRNA na kasar Iran ya nakalto ya nuna cewa wasu mutane a kan babur sun bude wutan bindiga kan wani mamba a dakarun kare juyin musulunci na kasar Iran wanda yayi sanadiyar shahadarsa.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - An kai hari kan Hassan Sayyid Khodaei ne a yau lahadi da misalin karfe 4 agogon Iran alokacin da jami’in yake kokarin shiga gida a cikin motarsa,dake gabashin kasar iran bayan da wasu mutake biyu akan babur suka harbeshi da bindiga har sau 5 da hakan ya yi sanadiyar rasuwarsa

Rahotan ya ci gaba da cewa harsashi guda 3 daga ciki sun same shi ne akai, yayin da guda biyu kuma suka harbe shi a hannu, bayanin da dakarun IRGC suka fitar jim kadan bayan afkuwar lamarin sun fadi cewa an kashe tsohon mamba din na IRGC ne a wani hari na ta‘addanci da wasu makiy jamhuriyar musulunci suka kai.

Wasu rahotanni sun bayyan cewa jama’an tsaro sun fatattaki maharani kuma sun fara gudanar da bincike kan lamarin.

342/