Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Lahadi

22 Mayu 2022

19:21:34
1259872

Iran : Ra’isi Zai Kai Ziyara Kasar Oman Ranar Litini

Shugaban kasar Iran Ibrahim Raisi zai kai ziyara kasar Oman, da nufin karfafa alakar da ke tsakanin kasashen biyu.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Iran da masarautar Oman na ci gaba da kulla alaka ta kut-da-kut, inda kasuwancin da ke tsakanin Tehran da masarautar Oman ya kusan ninkawa sau uku a cikin shekara guda, wanda ya kai na dala biliyan 1,3.

Oman ta taka rawa a cikin 'yan shekarun nan, wajen shiga tsakanin Iran da wasu kasashen Larabawa na yankin musamman Saudiyya.

Haka zalika ta shiga tsakanin Tehran da Washington musamman wajen musayar fursunoni da yarjejeniyar nukiliya.

342/