Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Lahadi

22 Mayu 2022

19:20:05
1259870

Sojin Burkina Faso Sun Hallaka Gwamman ‘Yan Ta’adda A Tsakiyar Kasar

Rundinar sojin Burkina faso ta sanar da dakile wani harin ‘yan ta’adda a barikin sojin Bourzanga, dake tsakiyar kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Sanarwar da rundinar ta fitar ta ce an hallaka ‘yan ta’adda kimanin talatin, saidai ta rara sojojinta guda biyar yayin artabun.

Sojojin sun kuma yi nasarar cafke makamai masu tarin yawa da babura da kuma motoci kirar pick-up da masu sulke.

Mayakan da ake alakantawa da na kungiyar GSIM, da aka kiyasta sun kai dari sun farmawa barikin sojin ne da asubahin ranar Asabar.

Burkina faso kamar sauren makobtanta na yankin Mali, da NIjar sun jima da suke fuskantar hare haren ta’addanci da ake dangantawa da na mayakan dake ikirari da sunan jihadi.

024