Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Sanarwar ta kara da cewa, wannan ziyara an shirya ta ne domin karfafa alakar da ke tsakanin kasashen biyu a fannoni daban-daban don cimma muradun kasashen biyu kawayen juna.
Wannan bayani ya yi nuni da cewa, a ziyarar da shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran zai kai kasar Oman a ranar gobe Litinin 23 ga watan Mayun shekara ta 2022 miladiyya, za a tattauna batutuwa da kuma abubuwan da suka dace a tsakanin kasashen biyu da ke makwabtaka da juna ta hanyar da za ta bayar da gudunmawa don cimma muradunsu da burinsu.
Baya ga haka kuma za a tattauna wasu batutuwa na kasa da kasa, da kuma na yankin, musamman halin da ake ciki a yankin tekun fasha, da kuma hanyar karfafa sulhu da fahimtar juna tsakanin gwamnatocin kasashen yankin.
342/