Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Lahadi

22 Mayu 2022

19:18:25
1259868

​Rasha Ta Haramta Wa Biden Da Wasu Amurkawa 962 Shiga Cikin Kasarta

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta fitar da jerin sunayen 'yan kasar Amurka 963 da aka haramtawa shiga kasar ta Rasha kwata-kwata, a matsayin martani ga irin wannan matakin da ita ma Amurka ta dauka.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - A cikin sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen kasar ta fitar ta ce: "A matsayin martani ga takunkumin da Amurka ke saka wa Rasha a kullum, ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta fitar da jerin sunayen 'yan kasar Amurka wadanda aka haramtawa shiga Tarayyar Rasha har abada. A cikin jerin sunayen mutanen da yawansu ya kai 963 har da Joe Biden, shugaban kasar ta Amurka."

Ma'aikatar harkokin wajen ta Rasha ta kara da cewa, "Muna jaddada cewa, matakan wuce gona da iri da Washington ke dauka kan Rasha ba za su taba wucewa ba tare da kwakkwaran martani ba, kuma wannan yana a matsayin somin tabi ne.

Bayanin ya kara da cewa, takunkuman Amurka da turai kan Rasha a matakin farko za su fara cutar da al’ummomin kasashen turan ne kamar yadda ake gani a halin yanzu, sannan kuma za su cutar da duniya baki daya.

Rasha dai ta sha jaddada cewa ba za ta taba bari Amurka da kungiyar tsaro ta NATO su yi amfani da wata kasa daga cikin kasashen da suke makwabtaka da ita domin cutar da ita ba, inda Rasha ta ce turawan sun fara yin amfani da Ukraine ne a matsayin zakaran gwajin dafi, kuma sun ga martanin Rasha kan hakan.

342/