Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Lahadi

22 Mayu 2022

19:14:44
1259866

​Sudan: Mutum Daya Ya Rasa Ransa A Zanga-Zangar Omdurman

Kwamitin tsakiya na likitocin Sudan ya sanar da cewa an kashe wani mai zanga-zanga a ranar jiya Asabar, yayin da yake halartar wani jerin gwano a birnin Omdurman, da ke yammacin babban birnin kasar, domin nuna adawa da juyin mulkin da sojoji suka yi.

Kwamitin ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa: jami’an tsaro sun amfani da harsasan bindiga masu rai wajen bude wuta kan masu zanga-zangar, inda suka kashe mutum guda da jikkata wasu da dama, inda yanzu haka ake kula da wasu daga cikinsu a asibiti.

Bayanin ya ce daga ranar 25 ga watan Oktoban day a gabata ya zuwa yanzu, jami’an tsaron gwamnatin sojin Sudan sun harbe mutane 96 har lahira, saboda sun nuna adawa da mulkin soji tare da yin kira da mika mulki ga hannun farar hula.

342/