Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Lahadi

22 Mayu 2022

19:13:16
1259865

Iran Da Omman Zasu Bunkata Aikin Tare Musamman A Bangaren Makamashi

Ministan man fetur na kasar Iran ya gana da tokwaransa na kasar Omman inda bangarorin biyu suka tattauna hanyoyin bunkasa dangantaka tsakanin kasashen biyu da musamman a bangaren makamashi.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa Javad Owji ya isa kasar Omman a jiya Jumma’a kuma ya gana da tokwaransa Muhammad Bin Hamad Al-Rumhi kan batutuwa da dama da suka hada kasashen biyu.

A makon da ya gabata ma yan kasuwan kasar Iran kimani 50 ne suka ziyarci kasar ta Omman don harkokin kasuwanci da kuma aiki atre don amfanin juna a bangarori daban daban.

A ranar litinin mai zuwa ne ake saran shugaban kasar Iran Sayyid Ibrahim Ra’eesi zai kai ziyarar aiki na farko zuwa kasar ta Omman. Inda ake saran zai gana da Sultan na Omman Haitham Bin Taroq Al-saeed. Inda ake saran ta shi da tawagarsa zasu tattauna batutuwan da suka shafi kasashen biyu musamman abinda ya shafi makamashi da kuma harkokin tsarin yankin Tekun farisa.

342/