Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Asabar

21 Mayu 2022

15:20:04
1259540

​Lavrov: Har Yanzu Faransa Tana Mafarkin Yin Mulkin Mallaka Kan Kasar Mali

Yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa da takwaransa na kasar Mali, Ministan harkokin wajen kasar Rasha ya yi gargadi game da halin da kasar Mali take ciki, sakamakon rikice-rikice da aka haifar a kasar, inda mayaka na kungiyoyin da ke dauke da makamai ba bisa ka'ida ba ke cin karensu babu babbaka a wasu yankunan kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Ministan harkokin wajen Rasha Sergey Lavrov ya bayyana hakan ne a jiya Juma’a, yayin da ya karbi bakuncin takwaransa na Mali Abdullah Diop a birnin Moscow, inda ya yi tir da tunanin mulkin mallaka na Faransa da Turai a kan kasar Mali.

Lavrov ya ce, rashin gamsuwar Faransa da bukatar mahukuntan Mali na neman taimako daga jami'an tsaron kasashen waje, ba komai ba ne illa bayyana tunanin mulkin mallaka, wanda kuma ya kamata Turawa su kawar da irin wannan tunanin daga kwakwalensu tun tsawon lokaci.

Ministan harkokin wajen kasar Rasha ya bayyana shirin Moscow na ba da goyon baya ga gwamnatin Bamako, wadda hukumar soji ke iko da ita, domin kara karfin jami’an tsaron kasar, musamman a fannin horar da sojoji da 'yan sanda.

A nasa bangaren, ministan harkokin wajen kasar Mali Abdoulaye Diop ya bayyana cewa, "hadin gwiwa tsakanin Rasha da Mali, a fannin soji, fasaha da siyasa, mataki ne mai kyau," ya kara da cewa ziyarar tamu a Moscow wata dama ce ta bayyana goyon bayanmu ga kasar Rasha.

342/