Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - A rahoton da jaridar Punch ta bayar, Babban bankin Najeriyar, ya yi amanna cewa, ƙananan kuɗade a halin yanzu basu da daraja sosai a kasuwa, bisa la’akari da farashin kayayyaki da kuma abin da za a iya saye da su a kasuwa.
Saboda haka ne Babban Bankin na Najeriyar ke ganin cewa, zai fi kyau a dakatar buga su, saboda maƙudan kuɗaɗen da ake kashewa wajen buga kananan kudaden, wanda hakan zai taimaka wajen rage kashe kudaden da gwamnati take yi ta wannan fuska.
Duk da haka, babban bankin ma Najeriya yace ya fito da tsarin E-Naira ne domin ya kasance an cimma tsarin kuɗi na bai ɗaya, kuma a samu tsarin kashe kuɗi ta hanya mai sauki ba tare da an yi mu’amala da tsabar kudin ba.
Darajar kudin Najeriya dai ta kara faduwa kasa warwars ne tun bayan amincewa da sharuddan asusun lamuni na duniya IMF da gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi, bayan da ta karbi makuden kudade na bashi, inda karya darajar Naira na daga cikin sharuddan da aka gindaya wa gwamnatin Buhari domin karbar wadannan basussuka daga wajen kasar, musamman ma daga bankin duniya da kuma asusun IMF.
342/