Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Asabar

21 Mayu 2022

15:18:38
1259538

​Rasha: Mayakan Ukraine Fiye Da 2,400 Sun Mika Wuya A Azovstal

Ma'aikatar tsaron Rasha ta sanar da cewa, sojojin Rasha sun kammala kwace iko da daukacin yankin rukunin masana'antu na Azovstal da ke Mariupol a kasar Ukraine, yayin da mayakan Neo-Nazi Azov na Ukraine da sojojin na Rasha suka killace su a wurin fiye da wata guda suka mika kai, daga ciki har da ma’akata.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Bayanin ya ce, "Rukunin karshe na 'yan Neo-Nazi Azov su 531 sun mika kai da makaman da ke hannun ga siojojin Rasha a jiya Juma’a, kamar yadda kakakin rundunar sojin Rasha, Manjo-Janar Igor Konashenkov ya bayyana a cikin wata sanarwa.

Ya kara da cewa, jimillar sabbin 'yan Nazi ko kuma Neo-Nazi Azov na Ukraine 2,439 da wasu mayakan na daban suka ajiye makamansu tun daga ranar 16 ga watan Mayu ya zuwa jiya 20 ga watan Mayu, kuma a halin yanzu daukacin rukunin Azovstal na karkashin ikon sojojin Rasha.

Ministan tsaron Rasha Sergei Shoigu ya sanar da shugaban Rasha Vladimir Putin a ranar Juma'ar cewa an samu nasarar kammala aikin, in ji Konashenkov. Ya kuma ce suna kula da dukkanin mayakan na Neo-Nazi Azov na Ukraine da suka shiga hannu, domin tabbatar da an kare lafiyarsu.

342/