Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Asabar

21 Mayu 2022

15:17:49
1259537

​Somalia: An Kama Wani Kwamanda Na Kungiyar Al-Shabaab

Dakarun Sojin kasar Somaliya sun kama wani daya daga cikin kwamandojojin kungiyar Al-Shabab mai alaka da Al-Qaeda, wanda ke da hannu a wasu tashe tashen hankula, an kuma cafke shi ne a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa Mogadishu babban birnin kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Wata majiya mai tushe ta bayyana cewa wanda ake tuhumar ya amsa laifinsa na kasancewarsa na kungiyar ta ta'addanci, kuma ya amsa cewa ya kai wasu bama-bamai a yankunan Janali, Bartiri, Zbeeb da kuma Afgoye, sannan kuma shi da kansa ya yi sanadin asarar rayukan fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba."

A daya bangaren kuma rundunar soji ta musamman ta sanar da kai wani farmaki na musaman a yankuna da dama a cikin gundumar Shabeele, da nufin kawar da ragowar 'yan ta'addar "Al-Shabaab" da suka yi saura a cikin yankunan.

Kungiyar ‘yan ta’adda ta Alshabab wadda take da alaka da kungiyar Alqaida, ita ce take daukar alhakin mafi yawan ayyukan ta’addanci da ake aikatawa a cikin kasar Somalia da sunan jihadi, wanda kuma tuni aka saka sunan kungiyar a cikin jerin kungiyoyin ‘yan ta’adda na duniya.

342/