Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Asabar

21 Mayu 2022

15:17:07
1259536

Iran Ta Shaidawa EU, Cewa Da Gaske Ta Ke Domin Cimma Yarjejeniya

Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta tabbatarwa Kungiyar tarayyar turai cewa da gaske ta ke domin cimma yarjejeniya mai karko a tattauanwar Vienna.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Wannan bayannin ya fito yayin wata zantawa ta wayar tarho da ta wakana tsakanin ministan harkokin wajen kasar ta Iran, Hossein Amirabdollahian, da kuma babban jami’in kula da harkokin ketare na kungiyar tarayyar turai Josep Borrell.

Yayin tattaunawar, Amirabdollahian, ya shaida cewa kasarsa na da kyakyawar niyya game da tattaunawar domin cimma yarjejeniya.

Bangarorin sun dai tattauna ne kan halin da ake ciki game da tattaunwar ta Vienna da kuma batun dagewa Iran takunkumi, dama wasu batutuwa da suka shafi kasa da kasa, ciki har da rikicin Rasha da Ukraine.

A nasa bangare shugaban kula da harkokin siyasa na kasashen turan, Josep Borrell, ya tabo batun shawarwarin da Iran, ta gabatar a tattaunawar ta Vienna, inda ya ce sun dukufa wajen ganin an ci gaba da tattaunawar domin samun mafita.

342/