Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Asabar

21 Mayu 2022

15:14:46
1259533

Habasha : Mayakan Tigray Zasu Sallami Fursunoni 4,206

‘Yan tawaye a yankin Tigray na Habasha sun bayyana anniyarsu ta sakin fursunonin yaki 4,206.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Daga cikin dakariun har da mata sama da 400 a cewar mayakan na Tigray.

Wata sanarwa da ofishin harkokin waje na yankin Tigray ya fitar ya bayyana cewa matakin ya zo ne bayan shiga tsakani da Kungiyar Tarayyar Afrika ta yi na kokarin kawo karshen yakin da aka shafe wata 19 ana yi.

Tsohon shugaban Najeriya Olesegun Obasanjo, shi ne ya jagoranci shiga tsakani a yankin na tsakanin mayakan na Tigray da gwamnatin Aby Ahmed.

342/