Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Jummaʼa

20 Mayu 2022

19:07:32
1259231

​Iran Ta Kaddamar Da Jirgin Saman Fasinja Na Farko Wanda Ta Bawa Suna Simorgh

Kamfanin kera jiragen sama na kasar Iran HESA ya kaddamar da karamar jirgin fasinja na farko kirar kamfaninn a jiya Alhamis.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa an gudanar da bikin kaddamar da samun jirgin fasinja ne a harabar kamfanin HESA dake birnin Esfahana a tsakiyar kasar. Sanna ministan tsaron kasar Iran Bugediya Janar Mohammad-Reza Ashtiani wanda ya kasance babban bako a bikin ya bayyana cewa wannan babban ci gabane ga kasar Iran. Don ana iya amfani da wadannan kananan jirage don bukatun cikin gida na fasinja da kuma harkokin tsaro kuma mataki ne na kere manya manyan jiragen saman fasinja da daukar kaya wadanda suka kai matsayin amincewa a fagen kasa da kasa.

342/