Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Jummaʼa

20 Mayu 2022

19:05:31
1259229

​Yake-Yake Da Musibin Dabi’a Sun Maida Mutane Kimani Miliyon 60 ‘Yan Gudun Hijira

Mutane kimani miliyon 60 ne suka kauracewa gidajensu saboda yake-yake da musibun dabi’a a shekara ta 2021 da ta gabata.

Shafin yanar gizo na labarai ‘Afriza News” ya nakalto kungiyoyin bada agaji da kare hakkin bil’adama daban-daban a duniya suna fadar haka a wani rahoton da suka fitar.

Rahoton ya kara da cewa mutanen da suke gudun hijira a cikin kasashensu sun kai miliyon 59.1 a shekara ta 2021 da ta gabata, kuma mafi yawansu yan kasa da shekaru 18 a duniya.

Kungiyar IDMC ta yan gudun hijira a cikin kasashensu ta bayyana cewa wannan adadin zai ci gaba da karuwa musamman sanadiyar yakin da aka fara a cikin watan Fabrairun wannan shekara a kasar Ukraine.

Daraktan kunghiyar ta IDNC Alexandra Bilak ta bayyana cewa shekara ta 2022 zata fi muni, sanadiyyar yakin da aka fara a Ukraine, don ya zuwa yanzu kadai mutane fiye da miliyon 8 ne suka kauracewa gidajensu a cikin kasar Ukrain watannin biyu kacal da fara yakin, a yayinda wasu miliyon miliyoyin sun sun shiga wasu kasashen Turai don neman mafaka.

342/